Ministan Tsaro, Dr Bello Matawalle, ya ce baje kolin kayayyakin tsaro na ƙasa da ƙasa na Afirka, AFRIDEX 2026, zai taimaka wajen bunƙasa masana’antar kera kayan tsaro a Najeriya da sauran ƙasashen Afirka.
Matawalle ya bayyana hakan ne yayin da aka fara baje kolin a Legas, wanda ya ce shi ne irinsa na farko tun bayan kafa Kamfanin Masana’antar Tsaro ta Najeriya (DICON) a shekarar 1964.
- APC za ta yi kamfe da nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu a zaɓen 2027 – Minista
- Sojoji sun fatattaki ’yan bindiga tare da kwato bindigogin AK-47 biyu a Benuwe
Ya ce an kafa DICON ne domin ƙera kayan aikin soja ga rundunonin sojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro, yana mai godiya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa jagorancinsa da kuma sanya hannu kan dokar DICON ta shekarar 2023.
A matsayinsa na shugaban kwamitin gudanarwa na DICON, Matawalle ya ce yana da aniyar ƙarfafa kera kayan tsaro a cikin gida, jawo masu zuba jari da kuma samar da damar musayar fasaha.
Ya ƙara da cewa waɗannan matakai za su taimaka wajen gina masana’antu domin tunkarar ƙalubalen tsaro a Najeriya da faɗin Afirka.