Shugaban jam’iyyar PRP, Hakeem Baba-Ahmed, ya yi gargaɗin cewa bai kamata a yi amfani da ibadar Umrah ko Hajji wajen neman goyon bayan siyasa ba.

A cikin saƙon da ya wallafa, Baba-Ahmed ya ce bai kamata a yi wa mutumin da ya je gudanar da Umrah ko Hajji mummunan zato game da niyyarsa ba.

Sai dai ya jaddada cewa bai dace mutum ya yi amfani da ibadun wajen neman goyon bayan siyasa ba, yana mai kira ga jama’a da su fahimci wannan batu.

Wannan furuci na zuwa ne bayan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gudanar da ibadar Umrah a ƙasar Saudiyya, inda ya kuma shiga cikin Ka’aba tare da tawagarsa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *