Gwamnatin Aljeriya ta bude wata Tashar samar da Wutar Lantarki a kauyen Gorou da ke jamhuriyar Nijar.
Shafin Jaridar Fitilar Nijar ya ruwaito cewa, Firaministan Aljeriya Siffi Ghrieb ne ya kaddamar da Sabuwar Tashar mai karfin Mega 40, da nufin wadata Birnin Yamai da kewayensa da hasken lantarki.
Firaministan Nijar Ali Lamine Zeine ne ya jagoranci bikin bude tashar a ranar Laraba, da nufin kyautata alaka tsakanin Nijar da Aljeriya.
Sai dai Shugaban Mulkin Sojan Kasar Janar Abdourahamane Tiani ya tashi zuwa Birnin Ankara domin ziyarar aiki ta kwanaki Uku, bisa gayyatar da shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan yayi masa.
A bayan Bayan nan dai alamu na nuna yadda kasar ke samun gagarumin sauyi ta fuskar kyautata alaka da kasashen waje.
Ko a ranar Talata 2 ga watan Yuni Sabon Shugaban Jamhuriyar Benin Romuald Wadagni ya kai ziyarar sabunta alaka Yamai, bayan da Nijar ta kulle kan iyakar ta shekaru Uku da suka gabata.
Gwamnatin Mulkin Soja a Jamhuriyar Nijar ta zargi tsohuwar Gwamnatin Shugaba Patrice Talon da marawa Faransa baya domin hambarar da gwamnatin Janar Abdurrahmane Tiani.
