Fiye da kashi 40 cikin 100 na mutanen da ke fama da ciwon sukari a duniya ba su san suna ɗauke da cutar ba, lamarin da ka iya hana su samun kulawar lafiya da magungunan da suke buƙata.

Ƙididdigar hukumar lafiya ta duniya ta nuna cewa yawan masu ciwon sukari a duniya ya ninka fiye da sau huɗu, daga mutum miliyan 200 a shekarar 1990 zuwa miliyan 830 a shekarar 2022.

Haka kuma, fiye da rabin masu cutar ba su yi amfani da magungunan da ake ba su ba a shekarar 2022.

Who ta ce ciwon sukari na iya haifar da manyan matsalolin lafiya da suka haɗa da makanta, gazawar ƙoda, bugun zuciya, shanyewar ɓarin jiki da kuma yanke gaɓoɓin jiki.

Ta ce fiye da kashi 95 cikin 100 na masu cutar na fama da nau’in ciwon sukari na biyu, wanda yanzu ake ƙara samun sa a tsakanin yara.

Alamomin cutar sun haɗa da yawan jin ƙishirwa, yawan fitsari fiye da yadda aka saba, ganin abubuwa cikin duhu, gajiya da kuma ramewa ba tare da shiri ba. Sai dai alamomin nau’in ciwon sukari na biyu na iya zama masu sauƙi, har mutum ya ɗauki shekaru kafin ya fahimci yana ɗauke da cutar.

Domin rage haɗarin kamuwa da cutar, ana shawartar jama’a su riƙa motsa jiki na aƙalla mintuna 150 a kowane mako, cin abinci mai gina jiki, rage sukari da kitse marar kyau, kiyaye nauyin jiki da kuma guje wa shan taba.

Hanya mafi dacewa ta gano ciwon sukari da wuri ita ce yin gwajin lafiya da na jini a kai a kai. Wannan na taimakawa wajen gano cutar tun da wuri da kuma fara samun kulawar da ta dace.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *