Wasu mutane da ake zargin an ɗauko su domin halartar taron jam’iyyar APC a Ibadan, Jihar Oyo, sun yi cacar baki da masu shirya taron bisa zargin kin biyansu cikakken kuɗin da aka yi musu alƙawari.

Bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna mutanen sun kewaye wata mota da ake zargin ta masu shirya taron ce, suna neman a biya su kuɗin da suka rage, tare da hana motar tafiya.

Mutanen sun yi zargin an yi musu alƙawarin Naira 5,000 kowannensu domin halartar taron, amma aka ba su Naira 2,000 kacal, inda suka ce ana bin su sauran Naira 3,000.

A cikin bidiyon, an ji wasu suna cewa ba za su bari motar ta wuce ba har sai an biya su kuɗinsu, yayin da waɗanda ake zargin masu raba kuɗin ne suka yi ƙoƙarin lallashin su, suna cewa kuɗin da suke da su ya ƙare.

Ba a tabbatar da waɗanda suka ɗauko mutanen ko kuma suka amince da biyan kuɗin ba, haka kuma babu wata sanarwa daga shugabancin APC a Oyo kan lamarin, ko bayanin ko an warware takaddamar.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *