Declan Rice, Gabriel da David Raya na daga cikin ‘Yan wasa Shida da aka zaba don karbar kyautar gwarzon dan wasan shekara na maza ta Kungiyar Kwararrun ‘Yan Wasan Kwallon Kafa.
Sauran sun hadar da dan Wasan Manchester United, Bruno Fernandes. Sai kuma ‘yan wasan Manchester City biyu da suka hada da Erling Haaland da Rayan Cherki.
A farkon wannan watan, Fernandes, mai shekara 31, ya lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na maza ta Kungiyar Marubuta labaran Kwallon Kafa.
Wannan kyautar galibi alama ce ta wanda zai fi cewar a ba shi kyautar gwarzon dan wasan shekara ta PFA.
- Najeriya da Poland sun yi canjaras a wasan sada zumunta
-
NFF ta fidda jadawalin wani Kwas na masu horaswa
Dan wasan tsakiyar Portugal din ya samu nasarar bayar da taimako ga abokan wasa 21 a gasar firimiya inda hakan ya taimakawa United kammalawa a matsayi na uku.
Dan wasan tsakiya Rice, mai tsaron baya, Gabriel da mai tsaron raga, Raya dukkansu sun kasance jiga-jigan ‘yan wasa a Arsenal, wacce ta lashe gasar firimiya a karon farko cikin shekara 22.
Dan wasan gaba na Man City, Haaland ya zura kwallaye 27 ya kuma lashe takalmin zinare(Ballon D’or) na gasar, yayin da Cherki ya samu nasara a kakarsa ta farko a gasar firimiya.
Tsohon dan wasan gefe na Liverpool Mohamed Salah ne ya lashe kyautar a bara bayan ya zura kwallaye 29 don taimakawa Reds lashe kofin firimiya.
Za a karrama wadanda suka yi nasara a ranar Talata, 25 ga Agusta a bikin bayar da kyaututtukan PFA na shekara karo na 53 da za a gudanar a garin Manchester dake Birnin Landan.
Wa kuke sa ran zai lashe kyautar PFA ta bana?