Mai dakin tsohon kakakin rundunar sojin kasarnan Hajiya Amina Abubakar ta roki gwamnatin jihar Katsina data sakar wa ‘yan bindigan wasu ‘yan uwansu dake tsare, kafin suma a sake su

Cikin wani bidiyo mai tsawon mintuna hudu da dakiku da yan bindigar suka saki a shafukan sa da zumunta, an ga mai dakin Tsohon Janar din tana mika wannan rokon ga gwamnatin jihar Katsina, da shuwagabannin wasu kananan hukumomin Jihar.

Amina ta ce Masu Garkuwar sun gindaya sharuddan sakin su da mai gidanta, matukar aka sakar musu  ‘yan uwa da suka hadar da Sani, Aminu da aka kama a karamar Hukumar Jikamshi, sai Nasiru da aka kama a Jihar Kano, tare da mayar musu da dabbobin su da aka kwace.

Da yake  magana a faifan bidiyon, Janar Rabe, ya nemi gwamnati tayi kokari don tabbatar da zaman lafiya, inda ya bayyana cewa masu satar sun nuna sha’awar yin sulhu da zaman lafiya.

Saidai duk kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu kan lamarin yaci tura, domin bai amsa kiranwayar da akayi masa ba.

Idan dai za’a iya tunawa a ranar Asabar 30 ga watan Mayun 2026 ne, wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da Manjo Abubakar Rabe mai ritaya, da mai dakinsa Hajiya Amina Abubakar, da kuma direbansu Abdullahi Sa’idu a daidai  kauyen Zakin Baure, dake kan hanyar Marabar Musawa–Kafinsoli, a karamar hukumar Matazu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *