Hukumar gudanarwar Jami’ar Tarayya ta Birnin Kebbi sun tabbatar da kisan wani dalibi, sai dai ba’a kai ga gane waɗanda suka kashe shi ba.
Ɗalibin mai suna Zaharadeen Nuhu, dake kan Shekarar karatu ta 3, ya rasa ransa a wani hari da ake zargin barayi ne suka kai inda yake.
Ana iya ganin munanan raunuka da suka haɗar da saran-Adda a jikin gawar.
Sai dai wasu na zargin ’yan daba da kai harin kan Gidan Kwanan ɗalibai dake wajen Jami’ar, a yankin Ƙaramar Hukumar Kalgo ta Jihar Kebbi.
Shugaban sashen kula da dalibai na jami’ar, Farfesa Ibrahim Magawata, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis kuma aka rabawa manema labarai a Birnin Kebbi.
-
Dalilan da suka jawo aka kafa Rediyo Najeriya Kaduna –Shugaban Jami’ar ABU
-
Mun rabawa dubban Almajirai Naman Sallah a bana -Hukumar kula da Almajirai
A cewar Magawata, marigayin, wanda ya fito daga Jihar Neja, ya shiga tarkon gungun wasu ɓata gari ne, bayan sunyi ƙoƙarin yi masa fashi a wajen Jami’ar.
Ta ƙara da cewa bayan garzayawa da shi asibiti daga bisani ya rasu a safiyar ranar Alhamis.
A saboda haka sanarwar ta shawarci dalibai da su taƙaita zirga-zirga a wasu lokuta, ko kuma tafiya cikin abokan karatu, tare da kai rahoton duk abinda basu gamsu da shi ba ga hukumar Jami’a.