Iran ta sake rufe mashigin Hormuz, a matsayin martani ga abin da ta kira karya yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin ta da Amurka.
Iran dai ta zargi Amurkan da gazawa wajen aiwatar da sashe na farko na yarjejeniyar wucin-gadi, da ke nufin kawo ƙarshen yaƙin da suke gwabzawa.
Sojojin Isra’ila sun yi artabu da mayakan Hezbollah yayin da jiragen yakin su ke kai hare-hare a kudancin Lebanon a ranar Asabar, sa’o’i kaɗan bayan Amurka ta sanar da sabunta yarjejeniyar tsagaita wutar rikicin
- Hare-haren Rasha a Ukraine sun lalata wuraren Ibada
- India: Wani hatsarin jirgi ya hallaka sojoji 5 a jahar Assam
- Afirka ta samu nasarar farko a gasar cin kofin duniya na 2026
Iran ta ce matukar bangarori basu girmama yarjejeniyar daina kaiwa Kasar Lebanon hari ba, ya zame mata dole sake daukar matakai da bai zama lallai suyi wa kowa dadi ba.
Kasar iran dai ta sanar da kulle mashigin ruwan ne a ranar 28 ga watan Fabarairun shekarar 2026, yayin da ta sake bayyana kullewa a ranar Asabar 20 ga watan Yuni, kasa da awanni 48 da budewa.