Kalaman baya-bayan nan da Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump, ya yi a birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya yayin Taron Masu Zuba Jari na Duniya (FII), sun yamutsa hazon fagen diflomasiyya.
Trump ya bayyana Afirka a matsayin “nahiyar da ke maƙare da arziƙin da ba a riga an taɓa ba,” yana mai kira ga ƙasashen duniya su kalli dimbin damar da ke cikinta.
Wannan yabo ya zo ne a daidai lokacin da gogayyar neman albarkatun Afirka ke ƙara zafi tsakanin Amurka da China da ƙasashen Turai.
Mujallar kasuwanci ta Business Insider ta ruwaito cewar kalaman na Trump a wannan lokaci sun zo da ba-zata, da tambayar shin wannan sabuwar soyayya ce ko kuma dabarar neman kaso a arziƙin nahiyar?
Sauyin fuska da muradin kasuwanci
Idan aka dubi tarihin maganganun Trump a shekarar 2018, inda ya yi amfani da kalaman batanci ga ƙasashen Afirka, sauyin muryarsa a shekarar 2026 na nuni da cewa Amurka ta fahimci ba za ta iya barin Afirka a hannun China da sauran ƙasashe ba.
Wannan yabo ba na kyauta ba ne; sako ne na gargadi ga sauran masu fafatawa a duniya cewa Amurka tana nan daram wajen neman kaso a arziƙin nahiyar.
Sannan maganar da Trump ya yi game da “arziƙin da ba a taɓa ba” na nuni da cewa nan gaba kaɗan, duk wata ƙasa da ba ta samu gindin zama a Afirka ba, to za ta rasa babban kashi na tattalin arziƙin duniya, musamman ta fuskar ma’adanai na fasahar zamani da makamashi.
Masharhanta na ganin wannan a matsayin babban kalubale ga shugabannin nahiyar, duk da cewa Trump ya jaddada buƙatar haɗin kai.
Shin ko shugabannin Afirka za su iya yin amfani da wannan gasa da ake yi a kansu don amfanin talakan nahiyar, ko kuma za su ci gaba da barin ta ta zama filin wasan manyan ƙasashe?
Lokaci ya yi da Afirka za ta tsaya da ƙafafunta don ganin an yi yarjejeniyoyin da za ta amfani kowanne bangare, domin fito da al’ummar ta daga duhun baƙin talauci.
Shin kuna ganin kalaman Trump na nuna girmamawa ne ga Afirka, ko kuma kawai yana son ya dakile tasirin China ne a nahiyar?
Ku ajiye mana ra’ayoyinku a sashen sharhi.
