Shugaban Majalisar Dattawa, Godwill Akpabio

Majalisar Tarayya ta amince da ƙarin wa’adin aiwatar da ɓangaren ayyukan raya ƙasa na kasafin kuɗin shekarar 2025 daga ranar 30 ga Yuni zuwa 30 ga Satumba, 2026, karo na uku ke nan da ake tsawaita wa’adin.

Majalisar Wakilai ta bayyana cewa matakin ya zama dole domin kauce wa dakatar da ayyukan da ake gudanarwa a sassa daban-daban na ƙasar. Shugaban masu rinjaye a majalisar, Hon. Julius Ihonvbere, ya ce rashin tsawaita wa’adin zai iya yin mummunan tasiri ga tattalin arziki da ci gaban ƙasa, yayin da Kakakin Majalisar, Hon. Tajudeen Abbas, ya ce bayanan da suke da su sun nuna cewa har yanzu ba a kammala aiwatar da kasafin ayyukan raya ƙasar ba.

Sai dai masu sharhi kan harkokin tattalin arziki sun nuna damuwa kan yadda tsawaita kasafin ya zama ruwan dare a Najeriya.

A cewarsu, ƙasar na gudanar da wasu ɓangarori na kasafin shekarun 2023, 2024, 2025 da 2026 a lokaci guda, lamarin da ke janyo matsalolin sa ido, gaskiya da kuma tantance yadda ake kashe kuɗaɗen gwamnati.

Rahotanni sun nuna cewa zuwa tsakiyar shekarar nan, an saki kusan kashi 20 cikin 100 ne kawai na kuɗaɗen ayyukan raya ƙasa na kasafin 2025, wato tiriliyan N4.99 daga cikin tiriliyan N24.9 da aka ware.

Haka kuma, wani rahoton Bankin Duniya ya bayyana cewa aiwatar da kasafin ayyukan raya ƙasa ya ragu duk da ƙaruwa a jimillar kashe kuɗaɗen gwamnati.

Masana sun danganta matsalar da yawan hasashen kuɗaɗen shiga da ba sa tabbata, da jinkirin tsarin saye da kwangila, da ƙarancin sakin kuɗaɗe ga ma’aikatu da hukumomi, da kuma matsalolin sa ido kan ayyuka.

Sun yi gargaɗin cewa idan ba a magance waɗannan matsaloli na tsari ba, da ci gaba da tsawaita kasafi zai ci gaba da zama alamar gazawar tsarin gudanar da kuɗaɗen gwamnati maimakon zama mafita ga ci gaban ƙasa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *