Gwamnatin Tarayya ta sanar da gano wani katafaren yankin ma’adanai masu tarin yawa a Jihar Kaduna, wanda ke ɗauke da ma’adanan dutsen platinum da zinariya da Farar Azurfa da jan ƙarfe da lithiyom  da kuma wasu muhimman ma’adanai da ake kira ‘rare earth elements’, wato sindaran Ƙasa da ba a fiye samun su ba.

Ministan Albarkatun Ma’adinai, Dele Alake ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin buɗe Taron Zuba Jari kan Albarkatun Ƙasa da Makamashi na nahiyar Afirka na shekarar 2026 da aka gudanar a Abuja.

Ya ce Hukumar Binciken Ƙasa da Ma’adanai ta Nijeriya (NGSA) ce ta tabbatar da binciken bayan wani kamfani mai zaman kansa ya gudanar da ayyukan bincike tare da haɗin gwiwar hukumar.

A cewarsa, yankin da aka gano na ɗauke da ma’adanai masu inganci da daraja da ake buƙata sosai a duniya wajen samar da makamashi mai tsafta, masana’antu da sabbin fasahohi.

Ya bayyana binciken a matsayin ɗaya daga cikin manyan nasarorin da aka samu a fannin haƙar ma’adanai a Nijeriya cikin ‘yan shekarun nan.

Ministan ya ce wannan ne karo na farko da gwamnati ke bayyana wannan bincike a hukumance, yana mai cewa hakan na nuna ci gaban da ake samu a ƙoƙarin gano sabbin ma’adanai a faɗin ƙasar.

Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da kamfanin Steron Mining and Company Limited ya bayyana cewa ya gano kimanin tan miliyan 3.3 na ma’adanin lithium a wurin haƙarsa da ke Abuja.

Alake ya ce gwamnatin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na aiwatar da sauye-sauye domin bunƙasa fannin ma’adanai, jawo jarin ƙasashen waje da samar da ayyukan yi.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *