Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta amince da Kasafin Kuɗin Shekarar 2026 wanda ya kai Naira tiriliyan 68.3.
Wannan adadi ya ƙaru da Naira tiriliyan 9 a kan Naira tiriliyan 58.4 da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar tun farko watan Disamba.
Shugaban Kwamitin Kasafi na Majalisar Dattawa, Sanata Olamilekan Adeola, ya ce ƙarin ya biyo bayan haɗa wasu muhimman ayyuka da ba a kammala ba a 2025, da kuma samar da wasu sababbin ayyukan more rayuwa.
Abubuwan da aka fi bai wa fifiko sun haɗa da sufuri, wato ginawa da sabunta hanyoyin jirgin ƙasa na zamani a jihohin Legas da Kano da Kaduna da Ogun; sai samar da hanyoyi a biranen Enugu da Maiduguri da ginin babbar hanyar Calabar zuwa Maiduguri da kuma hanyar Maiduguri zuwa Sakkwato.
Haka kuma kasafin ya kalli wani tsari na tallafa wa bangaren lafiya da kuma ware kuɗi na musamman ga kotunan ɗaukaka ƙara da Kotun Koli, a wani mataki na shirya wa shiga kakar zaɓe ta bana.
Gundarin kasafin ya nuna manyan ayyuka na kan gaba, inda za su lakume Naira tiriliyan 32.2.
Sai bashi da ake bin ƙasar nan wanda aka ware mishi Naira tiriliyan 15.8.
Ɓangaren gudanarwa zai lanƙwame Naira tiriliyan 15.4
A wani labarin kuma Majalisar ta amince wa Shugaba Bola Ahmed Bola Tinubu ya ciyo sabon baahi na Dala biliyan 6, bayan da ya aike mata da buƙatar hakan.
A cikin bashin da za a ciyo, za a karɓo Dala biliyan daga Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da nufin cike giɓin kasafin wannan shekara.
Sai kuma sauya basussukan da suka yi nauyi zuwa masu sauƙi.
Za kuma a karɓo ragowar Dala biliyan 1 daga HukumarLamunin fito ta Birtaniya, domin gyaran tashoshin jiragen ruwa na Legas da na Tin Can Island.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yaba wa matakin inda ya ce gyaran tashoshin jiragen ruwan zai sa Najeriya ta zama cibiyar kasuwanci ta duniya kuma zai bunkasa tattalin arziki.
Majalisar ta gargaɗi ɓangaren zartarwa da ya tabbatar an fitar da kuɗaɗen ayyukan a kan lokaci domin talakawa su gani a ƙasa.
