Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja a jihar Kogi ta soke wani hukunci da ta yanke a baya wanda ya umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta yi wa Jam’iyyar NDC rajista a matsayin jam’iyyar siyasa.

Mai shari’a, Isah Dashen ne ya yanke hukuncin a ranar Juma’a, inda ya bayyana cewa wajibi ne a saurari dukkan ɓangarorin da abin ya shafa kafin a yanke hukunci kan lamarin.

Kotun ta amince da bukatar Jam’iyyar PMP bayan ta bayyana cewa tana da ruwa da tsaki a shari’ar.

Alkalin ya ce hukuncin da aka yanke a watan Disamban 2025 yana da nakasu saboda ba a bai wa dukkan masu ruwa da tsaki damar kare matsayinsu ba.

Kotun ta kuma bayar da umarnin a mayar da komai yadda yake kafin hukuncin ranar 10 ga watan Disamban 2025, tare da umartar a sake fara sauraron shari’ar daga farko.

Lauyan Jam’iyyar PMP, Chikezie Ekeocha, ya ce sun garzaya kotu ne bayan gano cewa Jam’iyyar NDC ta yi amfani da tambarin da PMP ta gabatar wa INEC tun kafin a fara sauraron shari’ar.

Ya ƙara da cewa hukuncin na nufin dakatar da duk wani mataki da hukumar INEC ta ɗauka dangane da rajistar Jam’iyyar NDC, ciki har da takardar rajista da sanya jam’iyyar cikin bayanan hukumar, har sai an kammala sauraron shari’ar tare da haɗa dukkan ɓangarorin da abin ya shafa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *