Da ƙyar da jiɓin goshi, Brazil ta samu gurbin zuwa matakin ƙungiyoyi 16 na Gasar Cin Kofin Duniya bayan Gabriel Martinelli ya zura ƙwallo a mintin ƙarin lokaci.
Hakan ne kuwa ya tabbatar wa da Brazil ɗin nasara mai ban mamaki da ci 2-1 akan Japan.
Ƙasar Japan ce ta fara zura ƙwallo a ragar Brazil a rabin lokacin farko, ta hannun Kaishu Sano.
Bayan dawowa hutun rabin lokaci Brazil ta kara inganta salon wasanta, inda Casemiro ya farke ƙwallon da aka ci su a karon farko.
Shigowar ɗan wasan Arsenal Gabriel Martinelli daga benci ke da wuya ya ci ƙwallar da ta bai wa Brazil nasara a minti na 95, inda hakan ya faranta wa magoya baya rai a filin wasa na Houston.
Casemiro mai shekaru 34 da kwanaki 126, shi ne ɗan Brazil na biyu mafi tsufa da ya ci ƙwallo a Gasar Cin Kofin Duniya, bayan Bebeto kawai a 1998 (shekaru 34 da kwanaki 137 akan Denmark).