Air Marshal Sunday Kelvin Aneke

Babban Hafsan Sojin Sama na Nijeriya (CAS), Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, ya yabawa jami’an Rundunar Sojin Sama da ke ƙarƙashin Operation HADIN KAI tare da takwarorinsu na Rundunar Sojin Ƙasa bisa nasarar ceto ɗalibai da malamai da aka yi garkuwa da su bayan harin ‘yan ta’adda a Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Lassa, a Ƙaramar Hukumar Askira/Uba ta Jihar Borno

A cikin wata sanarwa da Daraktan Hulɗa da Jama’a da Yaɗa labarai na Rundunar Sojin Sama, Air Commodore Ehimen Ejodame ya fitar, Air Marshal Aneke ya bayyana cewa wannan nasara ta sake nuna ingancin ayyukan haɗin gwiwar hukumomin tsaro da ke amfani da sahihan bayanan sirri wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma tare da ci gaba da matsa wa ‘yan ta’adda lamba

Ya ce gaggawar tura jiragen leƙen asiri da sa ido (ISR), tare da bayar da tallafin hare-haren sama a kan lokaci, ya tarwatsa yunƙurin ‘yan ta’addan, wanda hakan ya bai wa dakarun ƙasa damar fafatawa da su tare da ceto waɗanda aka yi garkuwa da su

Ɗaya daga cikin waɗanda aka ceto, Mataimakin Shugaban Makarantar, Paul Namaske, ya bayyana cewa isowar jiragen soji ya sa ‘yan ta’addan suka watse, lamarin da ya bai wa malamai da ɗaliban da aka sace damar tserewa yayin da dakarun ƙasa suka kutsa zuwa inda ‘yan ta’addan suke.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *