Hukumar dake shirya damben (IBF) ta umurci dan Britaniya Moses Itauma, da ya shiga tattaunawa da dan kasar Cuba Frank Sanchez, kan fafatawa don lashe kambun na (IBF) da babu mai shi a yanzu.

A makon da ya gabata ne gwarzon dan damben Ukrain Oleksandr Usyk ya ajiye kambunan IBF, WBA ‘super’ da WBC.

Hukumar IBF ta ce, “a bisa ga dokokin gasar IBF”, tana son Sanchez, wanda ke lamba na daya a jerin ajin masu nauyi, ya fafata da Itauma, dake mataki na uku.

Hukumar ta kara da cewa suna da damar har zuwa 29 ga Yulin shekarar 2026, domin cimma yarjejeniya.

Itauma, mai shekaru 21, yana da shirin fafatawa da dan kasar Croatia Filip Hrgovic a filin wasa na O2 Arena dake Landan, a ranar 29 ga Agusta, abin da ya kira “fafatawar sa mafi wahala”.

Sai dai kuma yana da zabin janyewa daga fafatawar Hrgovic ko kuma ya amince ya fafata da Sanchez bayan wannan fafatawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *