Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Yakubu Ahmed, ya bayyana hakan yayin wata ziyara da ya kai hedikwatar Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) da ke Abuja.
Ya ce binciken da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) tare da rundunar ‘yan sanda suka gudanar ya nuna cewa ƙungiyar da ake kira “Yan Vocal” tana damfara da kuma karɓar kuɗi ta hanyar amfani da yanar gizo, ba ta da alaƙa da ayyukan ta’addanci.
A cewarsa, an riga an kama wasu daga cikin waɗanda ake zargi inda ya ƙara da cewa ƙungiyar da wasu ke kira “Sai Malam” ita ce wannan ƙungiyar Yan Vocal.
- NCDC ta ƙarfafa shirinta na dakile cutar Ebola a Nijeriya
- Gasar Kofin Duniya: Mutane Uku sun mutu a Mexico
Har ila yau, kwamishinan ya musanta rahotannin da ke cewa yara sama da 130 ne ke mutuwa a kullum a Jihar Kebbi sakamakon yawan mace-macen yara.
Ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya da aka ƙirƙira domin bata sunan gwamnatin Gwamna Nasir Idris gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Ahmed ya kuma ce Hukumar UNICEF ta tuntubi gwamnatin jihar, inda ta bayyana cewa rahoton da ake yaɗawa bai fito daga hukumar ba.
A nasa jawabin, Manajan Daraktan Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, Ali M. Ali, ya ce bunƙasar aikin jaridar jama’a da kuma amfani da fasahar basirar wucin gadi ta sauƙaƙa yaɗuwar labaran ƙarya.
Don haka ya buƙaci jami’an yaɗa labarai na gwamnati su riƙa fitar da sahihan bayanai cikin gaggawa domin dakile yaɗuwar labaran ƙarya.