Hukumar Babban Bankin Najeriya (CBN) ta soke lasisin gudanar da harkokin banki na bankunan Microfinance guda 46, yayin da ta naɗa Hukumar Kare Asusun Masu Ajiya ta Najeriya (NDIC) a matsayin mai kula da rushewa da rufe bankunan bisa tanadin dokokin BOFIA ta 2020 da Dokar NDIC ta 2023.

A cikin wata sanarwa da NDIC ta fitar, ta ce daga ranar 1 ga Yulin 2026 bankunan da abin ya shafa ba su da izinin ci gaba da gudanar da harkokin banki a Najeriya.

Hukumar ta yi gargaɗi ga jama’a da su guji yin kowace irin mu’amala da bankunan, tare da jan kunnen duk wanda zai yi yunƙurin ɓoye, kwashe ko lalata kadarori da takardun bankunan cewa hakan ya saɓa wa doka kuma zai iya jawo hukunci.

NDIC ta bayyana cewa ta riga ta fara karɓe da rufe bankunan cikin tsari, tare da tantance bayanan masu ajiya domin fara biyan waɗanda suka cancanci karɓar kuɗaɗensu da dokar inshorar ajiya ta tanada.

Hukumar ta kuma tabbatar wa masu ajiya da sauran jama’a cewa za ta ci gaba da sanar da su matakan da ake ɗauka yayin da aikin rushewa da biyan haƙƙin masu ajiya ke gudana.

Daga cikin bankunan da abin ya shafa akwai Gold MFB da Creditville MFB da Supreme MFB da Verdant MFB da Entrepreneur MFB da Now Now Digital MFB, da Bompai MFB da Kanopoly MFB da Bellbank MFB da Zain MFB da Ajwa MFB da Sycamore MFB da MBAG MFB da Casha MFB da kuma wasu da dama da ke jihohin Kano da Legas da Abuja da Kaduna da Kebbi da Ogun da Ribas da Abiya da Neja da Filato da Delta da Osun da Binuwai da Ondo da Oyo  da Cross River da Anambra.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *