Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta ce jami’anta sun ceto wata mata mai suna Adijat Kuburat mai shekaru 43 tare da ɗanta Abdul Malik Hamzat mai shekaru biyu, bayan da masu garkuwa da mutane suka sace su a jihar Kwara.
A cikin wata sanarwa, rundunar ta ce jami’an sashen tattara bayanan sirri na FID-IRT tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro na al’umma sun kai samame a wani daji da ke Bode Sadu a ranar Asabar bayan samun sahihan bayanan sirri kan inda aka tsare mutanen.
Sanarwar ta ce masu garkuwar sun buɗe wa jami’an wuta da suka hango su, sai dai jami’an sun mayar da martani, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa cikin dajin, kafin daga bisani aka ceto matar da ɗanta.
- Masu bauta da aka sace a Ekiti sun shaƙi iskar ‘yanci
- Amnesty ta buƙaci a yi bincike kan take haƙƙin ɗan Adam a kudu maso gabas
Rundunar ta ƙara da cewa an kai waɗanda aka ceto asibiti domin kula da lafiyarsu, yayin da ake ci gaba da farautar waɗanda suka tsere domin gurfanar da su a gaban shari’a.
Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu, ya yaba da ƙwazon jami’an da suka gudanar da aikin, yana mai jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da yaƙi da masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata miyagun laifuka a faɗin ƙasar.