Kylian Mbappe ya dawo cikin nishaɗi bayan ya ɓarar da bugun fenareti, inda ya zura ƙwallo mai ban sha’awa kuma ya taimaka wa Ousmane Dembele ya ci ƙwallo guda, yayin da Faransa ta tabbatar da shiga wasan kusa da na ƙarshe na Gasar Cin Kofin Duniya bayan ta doke Moroko 2-0 a filin wasa na Boston.

Mbappe shi ne ɗan wasa na farko da ya taɓa samun gudummawar ƙwallo 10 ko sama da haka a Gasar Cin Kofin Duniya sau biyu, tare da ƙwallaye 8 da bayar da taimako 3 a Gasar ta bana wanda ya zarce nasararsa ta 2022 (ƙwallaye 8, taimako 2).

A halin yanzu, Mbappe ya kamo Lionel Messi a gasar neman lashe takalmin Zinare na wanda yafi zura ƙwallaye na Gasar Duniya ta 2026, yayin da dukkaninsu suka zura ƙwalle 8.

Har yanzu, ya ƙara ƙaimi wajen kamo Messi na wanda ya fi zura ƙwallaye a tarihin Gasar Cin Kofin Duniya inda Messi ke da 21, shi kuma ya ke da 20.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *