Dakarun Operation HAƊIN KAI sun kama wata da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi daga ƙasar waje tare da ƙwace wani babban kaya na miyagun ƙwayoyi, barasa da sauran haramtattun abubuwa da ake zargin ana kai wa ƙungiyoyin ta’addanci da ke aiki a tsibiran Tafkin Chadi.
An kama wacce ake zargin ne a ranar Alhamis yayin wani samame da aka gudanar bisa bayanan sirri a kan hanyar Maiduguri zuwa Monguno a Jihar Borno.
An kama wacce ake zargin, mai suna Rachael Samuel, mai shekaru 48, ‘yar ƙasar Chadi daga garin Kelo da ke lardin Chari-Baguirmi, bayan da sojoji suka gano haramtattun kayayyaki a cikin motar..
- Mayaƙan ISWAP da iyalansu sun miƙa wuya – Sojoji
- Sojoji sun kama masu kai wa ‘yan ta’adda kayan tallafi
- Operation Haɗin Kai ta ceto ƙarin waɗanda aka sace, ta daƙile harin ISWAP a Borno
Mahukuntan soji sun bayyana cewa kayayyakin da aka ƙwace sun haɗa da damin tabar wiwi guda bakwai da aka matse, masu nauyin kusan kilogram 30, jarkoki biyu na lita 10 na sinadarin hydromercuric chloride, wanda aka fi sani da “Suck and Die”, kwalin da ke ɗauke da kwalabe 48 na busasshiyar giya (dry gin), da kuma kwalabe 61 na giya mai ganye.
Har ila yau, sojojin sun ƙwato wayar hannu, katunan ATM guda biyu, kuɗi da sauran kayayyakin sirri.
Wacce ake zargin na ci gaba da kasancewa a tsare a hannun sojoji, yayin da za a miƙa kayayyakin da aka kwace ga hukumar da ta dace domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da ita a gaban shari’a.
Rundunar ta kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanan sirri domin tallafa wa ƙoƙarin dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.