Gwamnatin Jihar Zamfara ta amince da bai wa ma’aikata mata hutun haihuwa na tsawon watanni shida, domin  samun damar kulawa da jariransu  tare da inganta lafiyar su.

Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Yakubu Haidara, ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis yayin da yake karɓar baƙuncin tawagar ƙungiyar (CS-SUNN) a Gusau.

Haidara ya bayyana cewa matakin da Gwamna Dauda Lawal ya ɗauka na nuna ƙudirin gwamnatinsa na yaƙi da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki da ke addabar yara, tare da inganta lafiyar jarirai a faɗin jihar.

Ya ce hutun haihuwa na watanni shida zai bai wa mata damar samun cikakken lokaci na murmurewa bayan haihuwa, rage haɗarin kamuwa da damuwar bayan haihuwa (postpartum depression), da kuma shayar da jariransu.

A cewarsa, wannan mataki zai kuma ƙara ƙarfafa alaƙar soyayya da kulawa tsakanin uwa da jaririnta tun daga farkon rayuwarsa.

Haidara ya ƙara da cewa gwamnatin jihar da ƙungiyoyin fararen hula suna aiki tare domin tabbatar da ingantacciyar lafiya ga yara da kuma samar da kyakkyawar makoma ga al’ummar jihar.

Ya tunatar da cewa a shekarar da ta gabata Gwamna Dauda Lawal ya amince da ware Naira miliyan ɗari biyar a matsayin kuɗin tallafi ga shirye-shiryen inganta abinci mai gina jiki, yana mai bayyana fatan cewa a wannan shekara ma gwamnatin za ta ci gaba da bayar da irin wannan tallafi ko ma fiye da haka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *