Manchester City ta kammala sanya hannu kan sayan Pierce Charles daga Ƙungiyar Sheffield Wednesday.
Ɗan wasan mai tsaron raga na kasar Arewacin Ireland ya sanya hannu kan kwangilar shekaru 5, wadda hakan zai ta ajiye shi a filin wasa na Etihad har zuwa shekara ta 2031.
Charles ɗan shekara 20, wadda babban yayansa Shea ya taɓa bugawa City wasa, ya kasance cikin Makarantar koyan Kwallo ta kungiyar kafin ya tafi Shefield Wednesday a bazara ta 2021 yana da shekara 16.
Bayan ya buga wasansa na farko a matsayin kwararre ga Shefield Wednesday a watan Janairun 2024, Charles ya buga jimillar wasanni 36 na manya ga ƙungiyar ta kudancin Yorkshire.
-
Kocin Morokoya yi alkawarin cewa tawagar za ta dawo da ƙarfi bayan ficewa daga Gasar Cin Kofin Duniya
-
Najeriya za ta karɓi baƙuncin Gasar Cin Kofin Ƙwallon Raga ta Rairayi ta Afirka ta 2027
Charles ya ce yana cikin farin ciki da dawowa City kuma yana matukar sha’awar fara sabon babi na aikinsa.
“Komawa Manchester City babban abu ne na musamman kuma abun alfahari ne gare ni da iyalina,” in ji shi.
Yanzu Charles zai koma Queens Park Rangers a matsayin ɗan wasan aro na tsawon kakar wasa ta 2026/27 baki daya.
“Zan ba da duk abin da zan iya don samun nasara a Gasar Championship kafin in dawo Manchester City,” in ji shi.