'Yar wasan Super Falcons,Toni Payne

Ƙungiyar ƙwallon ƙafar mata ta Italiya, Inter Milan, ya sanar da sanya hannu uku, sayan ‘yar wasan gaban Super Falcons, Toni Payne, kan kwantiragin shekaru uku abin da zai kai ta zuwa 30 ga watan Yunin 2028.

Nerazzurri sun tabbatar da zuwan ‘yar wasan ƙasar Najeriyan mai shekaru 30 bayan kammala kwantiraginta da ƙungiyar Everton ta Gasar mata ta Ingila.

An haifi Payne a ranar 22 ga watan Afrilu, 1995, a Birmingham, Alabama, kuma iyayenra ‘yan asalin Najeriya.

Bayan ta girma a Amurka, Payne ta koma Turai, inda ta buga wa ƙungiyar Ajax wasa kafin ta koma ƙungiyar Sevilla ta ƙasar Spaniya a shekarar 201; inda nan kuma ta yi shekaru 6.

Ta buga wasanni 168, a inda ta ci ƙwallaye 30.

Ta koma Everton ne a shekarar 2024, kuma yanzu za ta fara sabon babi a Italiya da Inter Milan gabanin kakar 2026/27.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *