Yara ashirin da babban mutum guda sun mutu a ranar Juma’a bayan motar bas da suke ciki ta kife a ƙasar Uganda.
Yaran, waɗanda suka fito daga King David Junior School da ke babban birnin ƙasar, Kampala, suna dawowa ne daga yawon shakatawa zuwa Sipi Falls da ke gundumar Kapchorwa, kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana.
A cikin wata sanarwa da suka wallafa a kafafen sada zumunta, ‘yan sanda sun ce “Ana zargin direban ya rasa ikon sarrafa motar, wadda ta kauce daga hanya, ta bugi wani babban dutse da ke gefen hanya, sannan ta kife.”
- Majalisar wakilan Amurka ta ƙaddamar da dokar rage tallafin waje ga Najeriya
- Rasha ta ayyana dokar ta ɓaci a yankin Crimea
- Amurka ta haramta wa duk wanda ya kasance a Congo cikin kwanaki 21 shiga ƙasar
Har ila yau, ‘yan sanda sun fitar da hoton motar bas ɗin, wanda ya nuna yadda ta lalace matuƙa sakamakon hatsarin.
Uganda na fama da matsalar rashin ingantaccen tsaro a hanyoyin mota.
A bara, wasu motocin bas biyu sun yi karo a wata babbar hanya a ƙasar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 46. A shekarar 2024 kuma, an samu haɗurran mota masu haddasa mutuwa har 4,434, inda jimillar waɗanda suka rasa rayukansu ta kai 5,144, kamar yadda wani rahoto ya nuna.