Hukumar NDLEA ta sanar da cewa ta samu nasarar rufe asusun banki da ke ɗauke da sama da Naira biliyan 9.8, waɗanda ake alaƙantawa da wata ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi.
Hukumar ta ce ta kuma samu umarnin kotu na wucin gadi na ƙwace wasu kadarori masu darajar biliyoyin naira, ciki har da gidan mai da manyan gine-gine da kuma motocin alfarma guda huɗu.
- Majalisar wakilan Amurka ta ƙaddamar da dokar rage tallafin waje ga Najeriya
- ‘Yan sanda sun ƙwato dabbobi 689 daga hannun ‘yan bindiga a Sakkwato
NDLEA ta bayyana cewa matakin ya biyo bayan binciken kuɗaɗen da ake zargin an samu daga harkokin miyagun ƙwayoyi, domin dakile hanyoyin da ƙungiyoyin masu aikata laifuka ke amfani da su wajen ɓoye dukiyoyinsu.
Shugaban Hukumar NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa mai ritaya, ya ce hukumar za ta ci gaba da bibiyar manyan masu safarar miyagun ƙwayoyi da kuma kadarorin da suka mallaka ta hanyar haramtacciyar hanya.