Rundunar Sojojin Najeriya ta sanar da cewa dakarunta sun daƙile wani hari da ‘yan bindiga suka kai tare da kwato shanaye 97 da tumaki 50 da aka sace a yankin Yankamaye–Rimaye da ke kan iyakar jihohin Kano da Katsina.
A cikin wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojin Najeriya, Manjo Babatunde Zubairu, ya fitar, an ce dakarun Joint Task Force Kano, tare da ƙarin jami’ai daga yankin mayar da martani, sun gudanar da aikin ne bayan samun sahihan bayanan sirri.
Sanarwar ta ce a ranar 15 ga Yuli, 2026, da misalin ƙarfe 5:45 na yamma, jami’an tsaro sun samu rahoton cewa wasu ‘yan bindiga na tafiya da dabbobin da suka sace ta yankunan Yankamaye da Rimaye. Nan take dakarun suka bazama tare da kafa shingaye a hanyoyin da ake zargin ‘yan bindigar za su bi.
- ‘Yan sanda sun ƙwato dabbobi 689 daga hannun ‘yan bindiga a Sakkwato
- Majalisar Wakilai: Abbas ya ba da shawarwari kan yadda za a kafa ‘yan sandan Jihohi
- Sarkin Musulmi Ya Ayyana Ranar Farko Ta Watan Safar 1448 bayan Hijira
Bayan kammala samamen, dakarun sun kama mutum biyu da ake zargi da ta’addanci, sannan sun kwato babur guda, shanaye 97 da tumaki 50.
Rundunar ta ce an mayar da dabbobin da aka kwato ga masu su na gaskiya.
Sai dai sanarwar ta bayyana cewa wani ɗan sa-kai mai suna Mallam Yusuf Adamu, mai shekaru 47 daga ƙauyen Yanchibi, ya rasa ransa bayan ya shiga tsakanin musayar wutar da aka yi.
Rundunar Sojojin Najeriya ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalansa da al’ummar ƙauyen Yanchibi, tare da bayyana lamarin a matsayin abin takaici.