Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta ayyana wani da ake zargi da jagorantar safarar miyagun ƙwayoyi, Nnamuka Kelvin Uchenna, wanda aka fi sani da Odogwu, tare da wasu mutum uku a matsayin waɗanda ake nema ruwa a jallo, bayan gano wata cibiyar ɓoye da ake ƙera sinadarin methamphetamine (meth) a jihar Imo
Hukumar ta kuma sanar da daskarar da kuɗaɗen da suka haura Naira biliyan 9.8 a wasu asusun banki da ake zargin suna da alaƙa da waɗanda ake nema, tare da samun umarnin kotu na wucin gadi na ƙwace kadarori masu darajar biliyoyin naira
- ‘Yan sanda sun kama masu garkuwa da masu bai wa ‘yan bindiga bayanai da masu safarar miyagun ƙwayoyi
- ‘Yan kasuwa na neman a farfado da matatun mai
- Tinubu ya ƙaddamar da rukunin samar da ruwa na Bwari, Ya yi kardadon faɗaɗa samar da ruwa a FCT
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar, an ce sauran waɗanda ake nema sun haɗa da Emmanuella Chinonso Iroka, Nnamuka Ifeanyi Kingsley, da Ekechi Franklin Chijioke, wanda aka fi sani da Ekene Okwunaga
Sanarwar ta ce Babbar Kotun Tarayya da ke Owerri, jihar Imo, ƙarƙashin Mai Shari’a Iniekenimi Nicholas Oweibo, ce ta bayar da umarnin ayyana su a matsayin waɗanda ake nema bayan NDLEA ta shigar da ƙara a ranar 3 ga Yulin 2026.