Zoben da FIFA za ta fara raba wa zakarun Gasar Cin Kofin Duniya.

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, ta sanar da cewa za ta fara baiwa tawagar da ta lashe Gasar Cin kofin Duniya ta 2026 zobe na zakaru a karon farko a tarihin gasar.

Wannan sabon tsari ne da FIFA ta samo daga al’adun wasannin Arewacin Amurka kamar NBA da NFL.

A cewar sanarwar, za a bai wa ‘yan wasa 30 na tawagar da ta lashe gasar zobuna na musamman waɗanda aka tsara, ban da kofin duniya da lambobin yabo na zakara.

FIFA ta ce an tsara zoben ne domin zama abin tunawa na dindindin kan nasarar da ‘yan wasan suka samu, da kuma bikin nasarar da suka samu a babban dandalin ƙwallon ƙafa ta duniya.

Hukumar ta kuma bayyana cewa za a fitar da wasu zobuna na musamman da adadinsu ya taƙaita domin magoya baya a fain duniya su samu damar mallakar wani yanki na abin tarihi na kofin duniya.

Gasar cin kofin duniya ta 2026 da Amurka, Kanada da Mexico su ke ɗaukar bakunta tare, ita ce za ta buɗe sabon al’adar bai wa zakara zobe na zakaru, wanda zai ƙara wani sabon salo ga gasar da aka faɗaɗa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *