Aikin shimfida bututun iskar gas na African Atlantic Gas Pipeline (AAGP), wanda aka fi sani da Nigeria-Morocco Gas Pipeline, na daga cikin manyan ayyukan makamashi da ake shirin gudanarwa a nahiyar Afirka a halin yanzu

Manufar aikin shine haɗa albarkatun iskar gas da Najeriya ke samar wa ga kasuwannin ƙasashen Yammacin Afirka da kuma nahiyar Turai, domin samar da sabuwar hanyar makamashi tare da ƙarfafa haɗin gwiwar tattalin arziki tsakanin ƙasashen nahiyar.

An tsara aikin ne domin shimfida bututun iskar gas mai tsawon kusan kilomita 6,900, wanda zai fara daga gabar Tekun Atlantika ta Najeriya, ya ratsa ƙasashe 13 na gabar teku a Yammacin Afirka, sannan ya isa Morocco kafin haɗuwa da kasuwannin Turai

Ana sa ran bututun zai iya ɗaukar kusan mita biliyan 30 na iskar gas (30 bcm) a kowace shekara.

Ba wai fitar da iskar gas zuwa ƙasashen waje kawai ake son cimmawa ba, domin aikin yana da manufar taimaka wa ƙasashen Afirka wajen samun makamashi mai yawa domin samar da wutar lantarki, bunƙasa masana’antu da kuma samar da taki.

A wani ɓangare kuma, ana sa ran iskar gas ɗin zata shiga kasuwannin Turai domin rage dogaro da wasu hanyoyin samar da gas.

Najeriya na kan gaba wajen cin gajiyar wannan aiki saboda yawan iskar gas da take da shi, wanda ya haura cubic feet tiriliyan 200.

Aikin zai ba ƙasar damar faɗaɗa kasuwannin iskar gas ɗinta, samun ƙarin kuɗaɗen shiga da kuma ƙara matsayinta a fannin makamashi na duniya.

Ga Morocco kuma, aikin zai ƙara mata damar samun ingantaccen makamashi domin amfanin masana’antu, da kuma ƙarfafa matsayinta na turbar haɗa Afirka da kasuwannin Turai.

Sauran ƙasashen Yammacin Afirka da yankin Sahel kamar Ghana, Senegal, Côte d’Ivoire, Mali da Nijar na daga cikin ƙasashen da ake sa ran za su amfana ta hanyar samun makamashin cikin sauƙi.

Haka kuma, ƙasashen da bututun zai ratsa za su iya samun kuɗaɗen shiga ta hanyar haraji da sauran harkokin tattalin arziki

Ana hasashen kuɗin aikin zai kai tsakanin dala biliyan 25 zuwa biliyan 27, kuma za’a gudanar da shi ta hanyar haɗin gwiwar gwamnatoci da kamfanoni masu zaman kansu.

Kamfanin mai na Najeriya, NNPC Limited, da hukumar makamashi ta Morocco, ONHYM, su ne manyan hukumomin da ke jagorantar aikin.

Za’a samar da kuɗaɗen gudanar da aikin ta hanyar haɗa jari daga masu ruwa da tsaki da kuma rancen kuɗi daga manyan cibiyoyin kuɗi na duniya, ciki har da bankunan ci gaban Afirka da sauran hukumomin da ke tallafa wa manyan ayyukan makamashi.

Ana shirin kafa cibiyar kula da manufofi da dokokin aikin a Abuja, Najeriya, yayin da za a kafa kamfanin gudanar da aikin karkashin AAGP Project Company a Casablanca, Morocco, domin kula da aikin.

Ana sa ran fara aikin a shekarar 2028, yayin da ake hasashen fara tura iskar gas ɗin a tsakanin shekarar 2031 zuwa 2033.

Kammala aikin na bututun iskar gas na African Atlantic Gas Pipeline zai zama ɗaya daga cikin manyan ayyukan samar da makamashi a tarihin Afirka.

Wanda zai haɗa albarkatun makamashin da nahiyar ke samar wa da kasuwannin duniya, tare da samar da sabbin damammaki ga tattalin arziki, masana’antu da samar da ayyukan yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *