Mataimakin Shugaban Ƙasar Najeriya, Kashim Shettima, ya ce dole ne ƙasashen Afirka su karɓi haƙƙinsu na mallaka da sarrafa albarkatun nahiyar tare da taka muhimmiyar rawa a kasuwancin duniya
Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a birnin Cotonou na Jamhuriyar Benin, yayin wata ziyara da tantancewa a Glo-Djigbé Industrial Zone (GDIZ).
- Sojojin Operation Haɗin Kai sun cafke masu garkuwa da mutane 5 a Yobe
- Mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba: Disu ya ba da umurnin fara samamen makonni 2 a Benue.
- Dole ne Arewa Maso-Gabas ta fi kowa aiki wajen yaƙar ta’addanci— Tinubu
Ya ce dole ne Afirka ta yi amfani da ɗimbin albarkatun ƙasarta ta hanyar bunƙasa masana’antun da za su sarrafa albarkatun ƙasa zuwa kayayyakin da ke da ƙima mai yawa.
Mataimakin shugaban ƙasar ya ce sabon ƙudirin gwamnatin Najeriya na bunƙasa masana’antu ba zai bar wata jiha ko yanki a baya ba, domin Gwamnatin Tarayya na aiki tare da gwamnatocin jihohi wajen cimma wannan buri.
Ya bayyana gamsuwarsa da ƙoƙarin da Jamhuriyar Benin ke yi wajen samar da kayayyaki da yawa tare da fitar da kayayyakin da aka sarrafa daga albarkatun cikin gida.
Shettima ya nuna taƙaicinsa cewa Afirka na cin moriyar kusan kashi ɗaya cikin ɗari (1%) ne kawai na masana’antar auduga ta duniya, wadda darajarta ta kai dala biliyan 370.