Turkiyya ta fada jimami da kaduwa ranar Laraba, bayan da wani dalibi ya bude wuta a wata makaranta dake Lardin Kahramanmaraş na gabashin kasar.
Rahotanni daga hukumomin tsaron Turkiyya sun tabbatar da cewa wani dalibi ne ya shiga makarantar da bindiga, inda ya bude wuta ba kakkautawa a azuzuwa dake hawa na biyu, lamarin da ya sanya dalibai da malamai tserewa domin ceton rayukansu.
Gwamnan Lardin, Mukerrem Unluer, ya ce maharin ya hallaka kansa bayan ya kashe wani malamin makarantar da wasu dalibai su biyu, sannan aka garzaya da mutane sama da 20 zuwa asibitoci mafi kusa domin ba su taimakon gaggawa.
Harin na ranar Laraba na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 bayan da wani tsohon dalibi ya jikkata mutane 16 a wata makarantar sakandare dake jihar Şanlıurfa dake kudu maso gabashin kasar ranar Talata.
Ministan Ilimin kasar Turkiyya, Malam Yusuf Tekin, ya ce gwamnati za ta kaddamar da bincike na musamman a kan yadda za a kara tsaurara matakan tsaro a makarantun kasar.
Rahotanni na cewa jerin hare-haren na sanya fargaba a zukatan iyaye da dalibai a fadin kasar Turkiyya, inda ake tambayar yadda aka yi bindigogi ke shiga hannun matasan cikin sauki.
