Atiku Abubakar ya ce ba a yi wa Arewa adalci ba a tsarin karba-karba

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya ce takarar da zai nema ta shugabancin kasa a 2027 ce ta karshe – daga ita ba zai sake tsayawa ba.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya fadi haka ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise.

“Neman zai fi zafi wannan karon domin ko tantama babu wannan ne karo na karshe”, inji Atiku.

Idan ya yi nasarar tsayawa a ADC, wannan ce za ta zama takara ta bakwai da Atiku, wanda yanzu shekarunsa na haihuwa 79, ya yi a yunkurinsa na darewa kujerar Shugaban Kasa.

Da aka tambaye shi ko ba ya ganin ‘’yan Najeriya suna bukatar sabon jini kuma za su yi mishi kallon tsohon yayi, sai ya ce yana wakiltar tsohon da sabon gaba daya.

“Mun ga matakai daban-daban na shugabanci a kasar nan”. a cewar Atiku, “matasa da dattawa duk mun gani – kuma na yi amanna rawar da matasa suka taka ba ta yi kyawun da muka zata ba.

Ni ina gani [matasan] suna bukatar kwarewa kuma suna bukatar jagora daga wurin dattawan”.

Ya buga misali da kwarewar da ya samu a karkashin Olusegun Obasanjo, yana cewa da bai yi aiki da tsohon Shugaban Kasar ba da ba zai koyi abin da ya koya ba.

Zan Hakura Da Takara Idan…

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya kuma ce rashin shugabancin da zai sa matasa a hanya ya taimaka wajen gazawar gwamnoni a jihohi da dama.

Game da yiwuwar ya janye wa wani mai neman takara da aka yi ittifaki a kansa kuwa, Atiku Abubakar ya ce akwai magana.

“Wannan ba maganar janyewa ba ce, [magana ce ta] zan goya [wa wani] baya?

“Matsayarmu a hadakar [ADC] ita ce a matakin farko mu samu yin ittifaki; idan hakan bai samu ba, sai mu yi zabe[n fid da gwani].

“Zan goyi bayan duk wanda aka yi ittifaki a kansa ko aka zabe shi”, inji Atiku.

Ya kuma ce a shirye yake ya goya wa dan takarar LP a Zaben Shugaban Kasa na 2023, Peter Obi, baya, in har shi jam’iyya ta zaba.

Karba-Karba

Da aka tambayi tsohon Mataimakin Shugaban Kasar game da batun karba-karba, sai ya ce ba a fahimci lamarin sosai ba.

“Ina ganin kuskure ne a ce akwai yarjejeniya game da batun karba-karba a Najeriya; bari ka ji – PDP ce kadai jam’iyyar da ta saka batun karba-karba a Kundin Tsarin Mulkinta.

“Saboda haka dukkan jam’iyyu ara suka yi suka yafa daga PDP — Idan kana maganar karba-karba ne tsakanin Arewa da Kudu a PDP, to ’yan Kudu sun yi shekara 18, yayin da ’yan Arewa suka yi 10.

“Idan za a yi adalci, wa aka tauye?”

Sai dai ya kara da cewa idan ya zama Shugaban Kasa zai tabbatar an yi wa Kundin Tsarin Mulkin Kasa kwaskwarima an shigar da batun karba-karba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *