Shugaban Majalisar Dattawa Godswill AkpabioShugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio

Yan Najeriya na cigaba da bayyana ra”ayoyinsu daban-daban a  kan kalaman Shugaban Majalisar Dattawa Godswil Akpabio, cewa matsalar tsaro a Najeriya ba za ta kau ba har sai an kammala zabubbukan 2027.

Dandalin X da Facebook ne shafukan da suke daukar kaso mafi rinjaye na ‘yan Najeriya musamman daga yankunan da rashin tsaro ya addaba kamar Kaduna da Katsina da Zamfara, sun nuna fushinsu game da kalaman.

Mutane da dama suna tambayar ko hakan na nufin za a ci gaba da zubar da jinin talaka ne har sai an kai lokacin zabe?

Wani mai amfani da dandalin Facebook ya rubuta: “Wato tsaronmu ya zama kayan cinikin siyasa? Idan har an san matsalar tana da alaka da zabe, me ya sa ba za a magance ta yanzu ba?”

A bangaren masu ruwa da tsaki, tsohuwar Ministar Ilimi Oby Ezekwesili tana cikin wadanda suka fara fitowa fili suna sukar kalaman, inda ta ce kalaman Akpabio suna nuna cewa akwai wata boyayyar manufa ta siyasa, sannan ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su sanya ido sosai a kan yadda ake amfani da batun tsaro wajen shirin zaben 2027.

Sai dai kuma a bangaren jam’iyyun hamayya, ana ganin kalaman a matsayin wata hanya da za ta taimaka musu kafa hujja da gazawar gwamnati mai ci wajen magance matsalar tsaro nan kusa, ko kuma a nuna wa al’ummar kasa cewar gwamnatin tana sane da abin da yake faruwa a harkar ta tsaro.

Yayin Babban Taron ADC na kasa, magabatan jam iyyar ta hamayya sun yi amfani da wannan dama wajen shaida wa mahalarta cewar gwamnatin APC tana amfani da matsalar tsaro domin raba kan al’ummar kasa kamar yadda take yi wa jam’iyyun adawa, domin juya alkaluman zabe mai gabatowa.

Masana tsaro suna ganin irin wadannan kalamai daga bakin wani babban jami’in gwamnati ka iya sanyaya gwiwar jami’an tsaro da suke fagen fama, tare da karfafa gwiwar masu laifi su ji cewa suna da kariyar gwamnati.

Masana suna ganin sau tari gwamnatoci kan nada shugabannin hukumomin tsaro bisa biyayya ga mahukunta maimakon kwarewa.

Hakan kan sanya hukumomin tsaro karkata wajen kare muradan gwamnati maimakon al’ummar kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *