Babban Hafsan Sojin Ƙasa (COAS), Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya sake jaddada aniyar Sojojin Najeriya na ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumomin agajin jin ƙai domin tabbatar da isar da tallafi cikin aminci a yankunan da rikice-rikice suka shafa, musamman a Arewa maso Gabashin ƙasar.

Shaibu ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin da ya karɓi bakuncin Shugabar Ofishin Hukumar Kula da Ayyukan Agajin Jin Ƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UN OCHA) a Najeriya, Danielle Parry, a Hedikwatar Sojojin Najeriya da ke Abuja.

Ya ce tabbatar da isar da agajin jin ƙai ba tare da cikas ba na daga cikin dabarun sojojin wajen ƙarfafa nasarorin da aka samu a yaƙi da ta’addanci da sauƙaƙa komawar ‘yan gudun hijira zuwa muhallansu da kuma tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.

Laftanar Janar Shaibu ya bayyana cewa Sojojin Najeriya za su ci gaba da samar da tsaro ga ma’aikatan agaji da motocin ɗaukar kayan tallafi da sauran kayayyakin jin ƙai, musamman a manyan hanyoyin da ake gudanar da ayyukan agaji.

Ya kuma amince cewa sake tsugunar da al’ummomin da rikici ya shafa da kuma rage cunkoson sansanonin ‘yan gudun hijira a Jihar Borno na tattare da ƙalubalen tsaro, amma ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da aiki tare da hukumomin agaji domin tabbatar da tsaron waɗannan shirye-shirye

A nata jawabin, Shugabar Ofishin UN OCHA a Najeriya, Danielle Parry, ta yaba wa Sojojin Najeriya bisa gudummawar da suke bayarwa wajen sauƙaƙa ayyukan agajin jin ƙai a Arewa maso Gabas.

Ta bayyana cewa kusan mutane miliyan shida har yanzu suna dogaro da agajin jin ƙai, yayin da tallafin da ake samu daga ƙasashen duniya ke ci gaba da raguwa.

Parry ta ce matsalolin tsaro a yankunan Gwoza da Bama da Damboa da Dikwa da Monguno na ci gaba da hana kai agaji yadda ya kamata, tare da roƙon sojoji da su ci gaba da ba da kariya domin bai wa waɗanda rikici ya raba da muhallansu damar komawa gonakinsu da sauran hanyoyin neman abin rayuwa.

Ta kuma buƙaci ƙarin tallafin sojoji wajen kawar da bama-baman da aka binne da sauran abubuwan fashewa da ba su tashi ba a yankunan da ake sake tsugunar da jama’a, da ƙara sintiri a manyan hanyoyin kai kayan agaji musamman a lokacin damina.

Parry ta jaddada cewa ci gaba da haɗin gwiwa tsakanin Sojojin Najeriya da hukumomin agajin jin ƙai na da matuƙar muhimmanci wajen kare rayukan fararen hula, kai agajin ceton rai da kuma tabbatar da zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa a yankin Arewa maso Gabas.

A watan yuni na 2015 rahoton Cibiyar Thomas Reuters Foundation yace rikin ‘yan kungiyar Boko Haram ya tilasta wa mutane sama da 800,000 barin muhallan su Arewa maso Gabashin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *