Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ya buƙaci sabbin jami’an masu gadin dazuka da aka horas da su su kare dazukan Najeriya tare da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ribadu, wanda Manjo Janar Hillary Mabeokwu ya wakilta, ya bayyana hakan ne a wajen bikin yaye jami’an da aka gudanar ranar Asabar a Cibiyar Muhammadu Buhari Civic Centre da ke Lokoja, Jihar Kogi.

Ya ce sabbin jami’an suna da muhimmin nauyi biyu, wato kare dazukan ƙasar da kuma ƙarfafa tsaro a al’ummomin da ke fuskantar barazanar ayyukan miyagun laifuka.

Ya sanar da cewa za a tura jami’an aiki nan take zuwa sassa daban-daban na jihar domin inganta tsaro da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Ribadu ya buƙace su da su gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa da mutunta haƙƙin ɗan Adam da kula da daidaiton jinsi da kuma bin ƙa’idojin aiki da dokokin ƙasa da ƙasa.

Ya ce gwamnatin tarayya ta kafa shirin masu gadin dazuka ne domin ƙarfafa tsaron ‘yan Najeriya, tare da kira ga jami’an da su yi aiki cikin gaskiya, jajircewa da riƙon amana.

A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta ƙarfafa tsaro a faɗin jihar, yana mai cewa ba za a bari wani yanki na dazukan Kogi ya ci gaba da zama mafakar masu aikata laifuka ba.

Ya ce bikin yaye jami’an ba wai ƙarshen horo ba ne kawai, illa alama ce ta sabon mataki na ƙarfafa tsarin tsaron jihar da tabbatar da cewa dazuka sun koma wuraren halastattun ayyukan tattalin arziki maimakon mafakar masu laifi.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta amince da horas da masu gadin dazuka 500 a Jihar Kogi, amma matasa 539 ne suka shiga shirin.

Bayan horo mai tsanani na tsawon makonni takwas, mutum 530 ne suka kammala horon kuma suna shirye domin fara aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *