Wata gobara ta tashi a ranar Lahadi a Terminal 2 na Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Murtala Muhammed da ke Jihar Legas.
Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN) ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na hukuma na X.
Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa FAAN, ta tura Sashen Ceto da Kashe Gobara na Filayen Jiragen Sama (ARFFS) domin shawo kan gobarar tare da hana ta yaɗuwa.
- Rukunin farko na dakarun wanzar da zaman lafiya sun isa Guinea-Bissau – NAF
- Ribadu ya bukaci sabbin masu gadin dazuka su kare al’ummomi cikin gaskiya da riƙon amana
- Jigawa – Gwamnati ta ware naira biliyan 13 domin magance zaizayar Ƙasa
Hukumar ta ce babu wani rahoton rasa rai ko jikkata sakamakon gobarar.
Sanarwar ta ce:”Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN) na sanar da jama’a cewa wata gobara ta tashi a Terminal 2 na Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Murtala Muhammed da ke Legas.
Sashen Ceto da Kashe Gobara na FAAN (ARFFS) na ci gaba da aiki a wurin domin shawo kan lamarin da kuma tabbatar da an kashe gobarar baki ɗaya.”