Shirin Majalisar Dattawa na binciken rahotannin binciken kuɗaɗe (Audit Reports) na shekarun 2021 zuwa 2023 kan harkokin man fetur da iskar gas da Hukumar NEITI ta gudanar ya fuskanci cikas a ranar Litinin, bayan wasu hukumomin da abin ya shafa sun gaza halartar zaman sauraron ra’ayoyin jama’a.

Hukumomin da aka gayyata sun haɗa da Babban Bankin Najeriya (CBN), Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC) da Hukumar Kula da Harkokin Haƙo Danyen Mai ta Najeriya (NUPRC).

Kwamitin Kula da Asusun Gwamnati na Majalisar Dattawa, ƙarƙashin jagorancin Sanata Ibrahim Dankwabo mai wakiltar Gombe ta Arewa, ne ya shirya zaman sauraron na tsawon makonni uku bisa rahotannin binciken da NEITI ta gabatar masa.

Sai dai da aka fara zaman, babu ko ɗaya daga cikin hukumomin uku da aka gayyata da ya halarta Haka kuma shugabanni da jami’an NEITI, wadda ta shirya rahotannin binciken, ba su bayyana ba.

Rashin halartar hukumomin ya fusata kwamitin, wanda ya umarci shugabannin CBN, NDDC da NUPRC da su tabbatar sun bayyana a gabansa a ranar Alhamis ta wannan makon ba tare da gazawa ba.

Da yake sanar da matsayar kwamitin, Sanata Dankwabo ya ce duk wata hukuma da ta sake ƙin halartar zaman da aka ɗage zuwa gare shi za ta fuskanci tsauraran matakan hukunci kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 da dokokin gudanar da aikin Majalisar Dattawa suka tanada.

Tun kafin kwamitin ya yanke wannan hukunci, ɗaya daga cikin mambobinsa, Sanata Babangida Hussaini, mai wakiltar Jigawa ta Arewa maso Yamma, ya buƙaci a aiwatar da tanade-tanaden kundin tsarin mulki da dokokin majalisar kan shugabannin hukumomin da suka ƙi amsa gayyatar majalisar.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *