Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Ƙasa, Mohammed Idris, ya bayyana cewa Tsarin ‘Renewed Hope’ (Sabon Fata) na Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana canza kyawawan manufofi zuwa ayyukan gani da ido, samar da ayyukan yi, sabbin fasahohi, da damammakin tattalin arziki a faɗin ƙasar nan.
Da yake jawabi a ranar Talata a babban ofishin Hukumar Kula da Kayan Aiki na Kimiyya da Injiniya ta Ƙasa (NASENI) da ke Abuja, yayin ziyarar Tawagar Yaɗa Labaran Shugaban Ƙasa a hukumar, Ministan ya ce an tsara wannan Ziyarar Kafafen Yaɗa Labarai ta Sabon Fata ta Ƙasa ne domin bai wa ‘yan Najeriya damar gani da idonsu ayyukan da shirye-shiryen da Gwamnatin Tarayya ke aiwatarwa.
“Muna son ’yan Najeriya su gani da idonsu yadda ake fassara manufofin gwamnati zuwa ayyukan gani da ido da ayyukan yi da sabbin fasahohi, da damammaki. Ana ƙarfafa gaskiya lokacin da hukumomin gwamnati ke tuntuɓar jama’a ba kakkautawa, sannan ana inganta riƙon amana lokacin da ‘yan ƙasa za su iya tabbatar da ci gaba da kansu,” in ji Ministan
Ya bayyana NASENI a matsayin wata babbar hukuma mai mahimmanci da ke jagorantar sauyin masana’antu na Najeriya ta hanyar kimiyya, injiniya, da fasaha, tare da tsoma baki da suka shafi masana’antun gida, makamashi mai sabuntawa da kayan aikin gona na zamani da fasahar dijital, da haɓaka ƙwarewa.
A cewar Ministan, hangen nesan Shugaba Tinubu shi ne gina tattalin arziki mai fa’ida da dogaro da kai wanda ya ginu a kan sabbin fasahohi da ƙara darajar kayan gida, da gasar masana’antu.
“Hangen nesanmu a bayyane yake: mu fitar da Najeriya daga zama ƙasa mai saye kawai da zama ƙasa mai samarwa, mai ƙirƙira, kuma mai fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje,” in ji shi.
Muhammad Idris ya lura cewa Tsarin Sabon Fata ya sanya bunƙasa masana’antu, fasaha, da rage marasa aikin yi a tsakanin matasa a tsakiyar sauyin tattalin arzikin ƙasa, ta hanyar samar da yanayi mai kyau don saka hannun jari, kasuwanci, da samar da ayyukan yi masu dorewa.
Ya jinjina wa shugabannin NASENI da ma’aikatanta saboda ciyar da fasahar gida gaba da kuma hanyoyin injiniya waɗanda ke ƙarfafa ƙarfin samar da kayayyaki na Najeriya tare da rage dogaro da shigo da kayayyaki daga ƙasashen waje.
Haka kuma Ministan ya yaba da mambobin Tawagar Yaɗa Labaran Shugaban Ƙasa saboda goyon bayan da suke ba wa gwamnatin tarayya wajen nuna gaskiya ta hanyar samar wa ‘yan Najeriya rahotanni na gaskiya, masu daidaito, da na gani da ido kan aiwatar da manyan shirye-shirye da ayyukan gwamnati. Bayan haka ne ya ƙaddamar da buɗe Ziyarar Tawagar Kafafen Yaɗa Labarai ta Shugaban Ƙasa a NASENI a hukumance.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *