Hukumar Babban Birnin Tarayya (FCTA) ta sanar da shirin ta na gina ƙarin tashoshin Motocin bas da tasi na zamani a faɗin Abuja, domin kawo ƙarshen haramtattun wuraren ɗaukar fasinjoji, inganta tsaron matafiya da kuma zamanantar da babban birnin.
Sakataren Hukumar Sufuri ta FCT, Mista Chinedum Elechi, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake yi wa manema labarai bayani a Abuja kan fara aiki da sabbin tashoshin bas da tasi da aka kammala a Mabushi da Gundumar tsakiyar Birnin wato (Central Business District)
- Takardar naɗin shugaban PFIPC ta bogi ce, ba daga Fadar Shugasa ta fito ba – ICPC
- Mauludin Shehu Tijjani: Shugaban Darikar Tijjaniyya na duniya ya sauka Najeriya
- ‘Yan Sanda sun gano maboyar ‘yan bindiga akan iyakar Filato da Bauchi
Ya bayyana cewa matakin da gwamnati ta ɗauka na kawar da wuraren ɗaukar fasinjoji ba bisa ƙa’ida ba, kamar Berger Junction da Area 1, na nufin dawo da doka da oda, kare rayuka da dukiyoyi da kuma inganta harkokin sufurin jama’a
A cewar sa, tashoshin Mabushi da Kugbo an tanade su ne domin tafiye-tafiye zuwa jihohin kasarnan, domin samar wa matafiya wadataciyya kuma amintacciyar hanyar sufuri, tsaron lafiya da walwala.
Elechi ya bayyana cewa kashi na farko na aikin ya haɗa da tashoshin Mabushi, Kugbo da Central District, yayin da aka riga aka saka shirye-shiryen ginin ƙarin tashoshi a cikin kasafin kudi na Hukumar anan gaba.