Sama da yara 300 ne suka mutu sakamakon cutar Ebola tun bayan barkewar cutar qa Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC), kamar yadda bayanan Majalisar Ɗinkin Duniya suka nuna.

Mataimakin kakakin Majalisar Ɗinkin Duniya, Farhan Haq, ya bayyana hakan ranar Juma’a, yana mai cewa ya dogara da alkaluman da Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya fitar.

A cewar Haq, yara na da kaso kusan ɗaya bisa huɗu na adadin waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar, amma suna da kusan ɗaya bisa uku na yawan mutanen da suka mutu sakamakon cutar.

Cutar ta Ebola na ci gaba da yaɗuwa cikin sauri a yankunan gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.

Adadin waɗanda suka kamu da cutar ya haura 4,000, yayin da aka ruwaito mutuwar mutane 1,850.

Barkewar cutar ta kuma kawo cikas sosai ga samun muhimman ayyukan kiwon lafiya. A yankunan da cutar ta fi kamari, amfani da ayyukan kiwon lafiya ya ragu da sama da kashi 40 cikin 100 a cikin watannin baya-bayan nan, yayin da tsoron kamuwa da cutar ke hana mutane zuwa asibitoci da cibiyoyin lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *