Hukumar Zaɓe ta kasa, ta ce ta kammala shirye-shiryen gudanar da zaɓen gwamnan jihar Osun da za a yi ranar Asabar 15 ga watan Agusta.
Hukumar ta ce an ɗauki matakan tsaro da na fasaha domin tabbatar da gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali, duk da yanayin tashin hankali da ake fama da shi a wasu sassan jihar.
Daraktar Wayar da Kan Masu Zaɓe da Hulɗa da Jama’a ta Hukumar, Victoria Eta-Messi, ta ce an gano wuraren da ake ganin ka iya fuskantar tashin hankali, kuma an tsara tura ƙarin jami’an tsaro zuwa irin waɗannan wurare.
Ta ce kwamitin haɗin gwiwa kan tsaron zaɓe, ya gudanar da tantance haɗarin tsaro domin gano wuraren da ke buƙatar ƙarin kariya,a cewarta, ‘yan sanda ne ke jagorantar ayyukan tsaro a lokacin zaɓen, yayin da sojoji za su samar da ƙarin tallafi a wuraren da ake buƙata.
Hukumar ta kuma ce ta yi aiki tare da ƙungiyoyin masu sufuri domin tabbatar da cewa ma’aikatan zaɓe da kayan zaɓe sun isa rumfunan zaɓe cikin lokaci.
Dangane da katin zaɓe na dindindin ta ce, ta tsawaita lokacin karɓar katunan tare da mayar da wuraren karɓar su zuwa matakin yin rijista.
Hukumar ta ce hakan, ya biyo bayan ƙarancin yawan mutanen da suka karɓi katunansu, musamman saboda ƙalubalen zuwa hedikwatar ƙananan hukumomi.Hukumar ta ce za ta samu cikakken adadin katunan da aka karɓa kafin ranar zaɓe, kuma bayanan za su taimaka wajen tantance sakamakon zaɓe da kuma yiwuwar gudanar da zaɓen cike gurbi idan tazarar ƙuri’u ta zama ƙasa da abin da doka ta tanada.
- Dan Takarar APC a Jihar Osun ya ce Jama’a su ne nasara shi
- Najeriya za ta kara da Afirka ta Kudu: Muhimman abubuwan da ya kamata ku sani
- Hukumar Zaɓe ta Ƙasa ta tura jami’an tsaro kimanin 25,000 jihar Osun
A gefe guda, Daraktan Fasahar Sadarwa da Bayanai na Hukumar, Dr Lawrence Bayode, ya kare aikin na’urar tantace kuri’a bayan matsalolin da aka samu yayin gwajin na’urar a ranar 1 ga Agusta.
Ya ce matsalar ta samo asali ne daga matakin kamanceceniya da aka sa wa tsarin tantance fuska, wanda ya yi tsauri ga wasu masu zaɓe, musamman waɗanda suka yi rajista tun shekarar 2011.
Ya ce an gano matsalar ne a lokacin gwajin kuma an gyara ta kafin ranar zaɓe.Dr Bayode ya kuma ce amfani da wayar hannu a na’urorin tantace kuri’a ba yana nufin cewa na’urorin ba su da tsaro,ya ce hukumar na amfani da ƙarin matakan tsaro na kanta wajen kare na’urorin.
A cewarsa, gwajin na’urar bai gaza ba, domin ya taimaka wajen gano matsalolin da ake buƙatar gyarawa kafin ranar zaɓe, kuma an samu nasarar tantance sama da mutum dubu ɗari yayin gwajin.
Za a gudanar da zaɓen gwamnan Osun a ranar 15 ga Agusta 2026, inda jam’iyyun siyasa za su fafata domin samun damar jagorantar jihar na tsawon shekaru huɗu.