Taswira ta Jihar Osun

A yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen gudanar da zaben sabon gwamna a Jihar Osun, a ranar Asabar, 15 ga watan Augustan 2026, wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullum Mr. Taofiq ya yi tsokaci kan matsalolin da suka dabaibaye jihar tare da yin kira ga duk wanda ya lashe zaben ya mayar da hankali wajen magance su.

Yayin zantawa da gidan Radiyon Blueprint a Abuja ranar Alhamis, Mr. Taofiq, ya ce babban abinda ke ci wa al’umma tuwo a kwarya shine rashin sakarwa kananan hukumomi mara wajen gudanar da ayyukan more rayuwa ga talakawan.

A cewar sa, “har yan zu ana shari’a a kotu akan batun kanann hukumomi waddda hakan ke hana shuwagabannin kananan hukumomi damar amfani da kudaden su wajen yi wa al’umma aiki.”

Masanin ya kara da cewa akwai bukatar hukumomi su aiwatar da manufofi dake karfafar matasa, shigar da su harkokin gwamnati ta hanyar ba su mukamai domin tallafawa wajen tafikar da sabbin manufofin dake bijirowa a zamanance.

“Ma fi akasarin abinda gwamnatoci ke yi shine baiwa matasa mukamin masu bayar da shawara, idan ka ga an baiwa wani mukamin Kwamishina sai wanda ya ke da shekaru ya dade ya na gwagwarmayar siyasa ko da bashi da kwarewa.”

Mr. Taofiq ya ci gaba da cewa akwai bukatar duk wanda ya lashe zaben gwamna a jihar ya yiwa al’ummar adalci, da kuma daina nuna fifiko tsakanin kananan hukumomin jihar, inda ya yi zargin cewa wasu kananan hukumomin suna samun ayyukan more rayuwa fiye da wasu.

”Ana nuna wa wasu kananan hukumomi wariya ta fannin gina yanyoyi, amma ba mu san dalilin yin hakan ba,” in ji shi.

A kokarin ta na tabbatar da yin adalci a zaben, INEC, ta ce ta fara sake buga takardun zaɓen gwamnan Jihar Osun domin saka sunan ɗan takarar jam’iyyar SDP, Dr Francis Olugbenga Ajala, da abokin takararsa Faseke Babajimi Oladipo.

INEC ta ce matakin ya biyo bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja na ranar 22 ga Yuli, 2026, wanda ya umarci hukumar da ta amince da Ajala a matsayin ɗan takarar SDP tare da sanya sunansa da bayanansa cikin takardun zaɓen.

Hukumar ta ce sabbin takardun zaɓen za su isa Jihar Osun a ranar Alhamis, 13 ga Agusta, sannan a rarraba su zuwa ofisoshin ƙananan hukumomi a jihar kafin zaɓen ranar Asabar.

Tuni dai Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta ce ta kammala shirye-shiryen gudanar da zaɓen, inda ta tabbatar da rajistar masu kaɗa ƙuri’a 2,339,233, a faɗin ƙananan hukumomi 30 da rumfunan rajista 332 da rumfunan zaɓe 3,763 a fadin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *