Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya bayyana cewa a tsarin mulkin da ya ginu kan dokokin Shari’a, amfani da kuɗaɗen jama’a wajen tallafa wa matasa masu buƙatar aure, wani mataki ne da ya dace kuma yana daga cikin kyakkyawan shugabanci.
Sheikh Gumi ya bayyana hakan ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya ce
“Yayinda karuwanci da zina da lalata da kuma rashin tarbiyya suka haramta a dokokin Allah da kuma dokokin gwamnati, yin amfani da kudaden jama’a don taimaka wa aurar da mata da suka fi yawa fiye da yawan mazajen da suka cancanci aure, ko kuma duk wani matashi da yake cikin tsananin bukatar yin aure, wani mataki ne halastacce kuma alama ce ta kyakkyawan shugabanci”
- Musulmi da Kiristoci sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Abuja
- Gwamnati za ta rufe karɓar ra’ayoyi kan dokar kafa ’yan sandan jihohi
- ‘Yan takarar dake kan gaba a zaben gwamnan jihar Osun
A cewarsa, tallafa wa aure ta hanyar amfani da dukiyar jama’a ga waɗanda suke cikin tsananin buƙatar yin aure na iya zama hanya ta kare tarbiyyar al’umma da ƙarfafa zaman lafiya.
A na dai kallon kalaman nasa a matsayin martani ga masu sukar auran gata da gwamnatin jihar Kano ta shirya a karshen makon da ya gabata, in da gwamnatin ta aurar da samari da zawarawa 1,500.