Almajirai huɗu na Tsangayar Malam Iliyasu Mai Tsangaya da ke Kadage Sharifai a Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano sun rasu bayan cin abincin da ake zargin gurɓatacce ne.
Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Shugaban ƙungiyar Tsangaya Media Network ta ƙasa, Alaramma Sani Musa Nuhu, ya fitar.
- Cardoso, Ojulari, Tantita za su karɓi lambobin yabo na Blueprint Newspapers
- Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Edo ya yi murabus
- Wani Fasto ya karrama wani malamin Addinin Musulunci a Najeriya
Sanarwar ta ce, almajiran sun rasu ne a Asibitin Malam Aminu Kano a daren Lahadi, 16 ga Agusta, 2026, bayan sun ci abincin da ake zargin ya gurɓata.
Sanarwar ta ƙara da cewa, an gudanar da jana’izar almajiran bayan samun umarni daga Dagaci da baturen ƴan snadan yankin.