Iran ta sanar da bayar da lada da ya kai dala 30,000 ga duk wanda ya kashe ko ya kama wani sojan Amurka, yayin da za a ninka ladan zuwa dala 60,000 idan mace ce ta aikata hakan.
Shugaban sojojin Iran, Amir Hatami, ya ce an tsara wannan shiri ne bayan da aka samu “buƙatu masu yawa” daga mutanen da ke son shiga cikin aikin, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Iran na IRNA ya ruwaito.
Sai dai ba a san cewa Amurka ta tura sojojin ƙasa zuwa cikin Iran ba tun bayan barkewar yaki, da wani samame na ceto da aka kai a watan Afrilu domin kwace wani sojan saman Amurka da jirginsa ya faɗi. Hatami bai bayyana inda ko lokacin da ake sa ran kai hare-haren kan sojojin Amurkan ba.
Hatami ya ce duk wanda ya kashe ko ya kama wani sojan Amurka da Iran ke kallon a matsayin mai leƙen asiri sannan ya mika shi ga hukumomin Iran, zai samu ladan dala 30,000 ko kuma biliyan biyar na toman. Ya kuma ce matan Iran masu ƙarfin hali da suka aikata hakan za su samu ladan da aka ninka.
- Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Edo ya yi murabus
- Wani Fasto ya karrama wani malamin Addinin Musulunci a Najeriya
- FLA ta saki sojojin Mali da suke fama da raunuka
Shugaban sojojin ya sake yin kira ga Amurka da ta fice daga Gabas ta Tsakiya. Ya ce sojojin Amurka ba su da izinin shiga Tekun Fasha, Tekun Oman ko mashigar ruwan Hormuz.
Yakin Iran da Amurka ya fara ne a ranar 28 ga Fabrairu, bayan da Amurka da Isra’ila suka kai hari kan Iran. Bayan kusan kwanaki 40 na gwabza fada, an cimma tsagaita wuta a watan Afrilu, sannan aka tsara wani tsarin tattaunawar zaman lafiya a watan Yuni, amma daga bisani tattaunawar ta wargaje.
Tun daga lokacin, kasashen biyu sun rika musayar wuta lokaci-lokaci, musamman a kudancin Iran da yankin mashigar Hormuz.
A halin yanzu, ana ci gaba da tuntubar juna a fakaice ta hannun masu shiga tsakani, duk da cewa babu wata alama mai ƙarfi ta samun ci gaba a diflomasiyya.
Iran ta kuma gabatar da wasu sharudda kafin a sake bude mashigar Hormuz, ciki har da biyan diyya kan barnar yakin.
Adadin sojojin Amurka da aka ce an kashe tun farkon yakin ya kai 17, kuma na baya-bayan nan sun mutu a watan Yuli. Dukkaninsu an kashe su ne a wajen Iran, ciki har da Jordan da Iraki.