Shugaban ƙungiyar Galatasaray, Dursun Ozbek, ya shaida wa Arsenal cewa Victor Osimhen ba na sayarwa ba ne, kamar yadda kafar sadarwa ta football.london ta ruwaito.
Ana danganta Gunners da yunƙurin siyan ɗan wasan gaba na Najeriya, yayin da Mikel Arteta ke neman sabbin ‘ƴan wasan gaba don ƙarfafa tawagar zakarun Gasar Firimiyar Ingila.
Ko da yake, Arsenal ta sayi Bruno Guimaraes kuma ta kawo Christos Tzolis don maye gurbin Leandro Trossard, amma ta kasa samun Vinicius Junior da Morgan Rogers.
-
Bruno Fernandes ba na sayarwa ba ne
-
Awoniyi zai koma Coventry
-
Yadda Kamaru ta lashe kofin Gasar WAFCON ta 2026
Rahotanni sun ce Arsenal ta mayar da hankalinta zuwa kan Osimhen yayin da damar samun Julian Alvarez na Atletico Madrid ke raguwa.
Rahoton kafar 343 Digital ya ce Ozbek ya shaida wa mutanen cikin ƙungiyar cewa: “Ba zan iya ce ‘eh’ akan wani kasuwanci da zai cutar da Galatasaray ko wadda ba za ta amfane ta ba. Abin da na faɗa game da Baris Alper Yilmaz, shine zan sake faɗi da ƙarfi game da Osimhen. Ko wani irin farashi ne, ba zan sayar da Osimhen ba.”
Ba abin mamaki ba ne shugaban na Istanbul ya ci gaba da riƙe ɗan wasan gaban, bayan ya zura ƙwallaye 22 a dukkan fafatawa a kakar da ta gabata.
Osimhen ya ci ƙwallaye 15, yayin da Galatasaray ta lashe kofin Gasar Turkiyya a bara, kuma ɗan wasan mai shekaru 27 ya taka muhimmiyar rawa a wasansu na farko a ƙarshen mako.
Sai dai Osimhen bai ɓoye burinsa na son taka leda a Gasar Fimiyar Ingila ba, lokacin da ƙungiyar Chelsea ta nuna sha’awar sayan dan wasan a 2023.
