Rashin halartar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya jawo hankali a taron farko na rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin ’yan takarar shugaban ƙasa gabanin zaɓen 2027.
An gudanar da taron ne a Abuja domin haɗa kan ’yan takara da sauran masu ruwa da tsaki, tare da samar da fahimtar juna kan buƙatar gudanar da yaƙin neman zaɓe da babban zaɓen 2027 cikin lumana da bin ƙa’ida.
Daga cikin manyan ’yan takarar da suka halarci taron akwai Peter Obi na jam’iyyar NDC da Omoyele Sowore na AAC, yayin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ɗan takarar APC, ya samu wakilcin Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume.
Sai dai abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne rashin halartar Atiku Abubakar, wanda ke cikin fitattun ’yan takarar da ake sa ran za su taka muhimmiyar rawa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Rahotanni sun ce Atiku bai halarci taron ba, kuma bai tura wani wakili da zai wakilce shi ba.
Sai dai jam’iyyar ADC ta ce shugaban jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya halarci taron.
A yayin taron, ’yan takara da sauran masu ruwa da tsaki sun jaddada muhimmancin gudanar da harkokin siyasa cikin lumana, tare da guje wa kalaman da za su iya haifar da tashin hankali kafin da lokaci da kuma bayan zaɓe.
- Zaɓen 2027: Yan takarar shugaban ƙasa sun rattaba hannu kan yarj
- Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa a taron bada lambobin girma na Blueprint karo na 8.
- Taron lacca da Karrama wasu Muhimman mutane na shekara -shekara na Jaridar Blueprint.
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, da jami’an tsaro su ma na daga cikin waɗanda suka halarci taron, inda aka tattauna kan matakan da za su taimaka wajen tabbatar da ingantaccen tsarin zaɓe mai cike da zaman lafiya.
Kwamitin Zaman Lafiya na Ƙasa, ƙarƙashin jagorancin tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ne ya shirya taron tare da haɗin gwiwar cibiyar Kukah.
Yayin da rattaba hannu kan yarjejeniyar ke nuna aniyar ’yan siyasa na gudanar da zaɓen 2027 cikin lumana, rashin halartar Atiku Abubakar ya ƙara jawo tambayoyi kan yadda dukkan manyan ’yan takarar za su kasance cikin wannan tsarin na tabbatar da zaman lafiya.
Yanzu hankali ya karkata kan matakin da sauran ’yan takara za su ɗauka wajen tabbatar da cewa yarjejeniyar ba ta tsaya a kan rattaba hannu kawai ba, illa ta zama alkawarin da za a aiwatar kafin, lokacin da kuma bayan zaɓen 2027.