An naɗa fitaccen malamin addinin Musulunci ɗan Najeriya, Farfesa Bashir Aliyu Umar, a matsayin Shugaban Majalisar Ba da Shawara kan Harkokin Kuɗaɗen da Ba Su da Riba NIFAC ta Babban Bankin Ghana.
Ana sa ran Majalisar NIFAC za ta bai wa Babban Bankin Ghana shawarwari kan yadda za a bunƙasa da kuma tsara dokokin harkokin kuɗaɗen da ba su da riba a ƙasar.
Ayyukan majalisar za su fi mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi kyakkyawan shugabanci da tsara dokoki da kuma tabbatar da bin ƙa’idojin Shari’a a fannin kuɗaɗen da ba su da riba.
- Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada aniyar gudanar da Zaɓukan 2027 cikin tsaro da gaskiya — Ministan Yaɗa Labarai
- Zaɓen 2027: Yan takarar shugaban ƙasa sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya
- NDLEA ta yi kamun Hodar Iblis mafi nauyi a tarihin kafuwar ta
A matsayinsa na shugaban NIFAC, ana sa ran Farfesa Umar zai yi amfani da ƙwarewarsa wajen taimakawa wajen samar da ingantaccen tsarin dokoki da zai tafiyar da cibiyoyin kuɗi da kayayyakin hada-hadar kuɗaɗe da ba su da riba a Ghana.
Haka kuma, aikinsa zai haɗa da taimakawa wajen tabbatar da cewa ayyukan kuɗaɗen da ba su da riba sun yi daidai da ƙa’idojin Shari’ar Musulunci, tare da bin dokokin da hukumomin Ghana suka tanada.
Farfesa Bashir Aliyu Umar ya shahara wajen gudummawar da yake bayarwa a fannin ilimin addinin Musulunci, musamman a harkokin kuɗaɗen Musulunci da karatun da ya shafi Shari’a.
Ayyukansa na ilimi da kuma gudummawarsa a fannin kuɗaɗen Musulunci sun zarce iyakokin Najeriya, inda ya samu karɓuwa a tsakanin masana da masu ruwa da tsaki a fannin kuɗaɗen Musulunci na duniya.
Naɗin ya jawo taya murna daga mambobin al’ummar masu ruwa da tsaki a fannin kuɗaɗen Musulunci, waɗanda suka bayyana shi a matsayin wata babbar nauyi ta ƙasa da ƙasa da aka ɗora wa malamin ɗan Najeriya.